Ya yin zantawar su shugaba Xi ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta matasa ta hade wasannin motsa jiki, da al'adu, da ilimi guri guda. Ya ce baya ga wasanni, wannan gasa ta zama wani dandali na mu'amalar kasashen duniya. A sabili da haka, gasar za ta taka muhimmiyar rawa wajen yada tunanin Olympics, da ba da jagoranci ga matasa wajen yin la'akari da hanyar rayuwa, da kuma ra'ayin gudanar da irin rayuwar da ta dace, baya ga sada zumunta a tsakanin daukacin fannoni baki daya.
Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin na baiwa wannan gasa cikakken muhimmanci, ta yadda za ta zamo mai alamar musamman ta Sin.
A nasa bangare, mista Thomas Bach ya bayyana cewa, kwamitin wasannin Olympics na duniya yana kokarin yada tunanin Olympics a duniya baki daya, da zummar sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da samun dauwamammen ci gaba a duniya, ta hanyar amfani da wasannin motsa jiki.
Mr. Bach y a ce kwamitin na darajanta hadin gwiwa tsakaninsa da Sin, ya kuma jinjinawa kasar Sin, game da irin muhimmancin da take baiwa bunkasar sha'anin wasannin motsa jiki, da irin rawar a zo a gani da take takawa a fannin wasannin na Olympics a mataki na duniya.(Fatima)