in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a yi bikin bude gasar Olympics ta matasa a birnin Nanjing
2014-08-15 20:23:32 cri
A ranar 16 ga wata ne za a yi bikin bude gasar wasannin Olympics ta matasa ta lokacin zafi karo na biyu a birnin Nanjing dake kudancin kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping zai halarci bikin tare da sanar da fara gasar a hukunce.

'Yan wasa sama da 3700 da suka zo daga kasashe daban-daban ne ake saran za su halarci wasannin guda 222 da za a fafata a kansu, inda za a kashe kwanaki 12 ana yinsu, a sa'i daya kuma, za a gudanar da wasu shirye-shiryen al'adun da abin ya shafa a yayin gasar. Haka kuma, kwamitin gasar wasannin Olympic na kasa da kasa na fatan matasan kasa da kasa za su iya shiga cikin wasannin motsa jiki cikin himma da kwazo, kuma yana fatan matasan kasa da kasa da su iya yin zaman duniya tare da bin akidar Olympic. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China