in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da bukukuwan al'adu fiye da 70 a birnin Nanjing a yayin wasannin Olympics na matasa
2014-08-12 14:45:29 cri
Kwamitin wasannin Olympics na matasa na birnin Nanjing na kasar Sin ya sanar da cewa, a yayin wasannin Olympics da birnin zai karbi bakunci, za a gudanar da bukukuwan al'adu 77, domin nishadantar da matasa da za su halarci bikin daga sassan duniya daban daban.

Kaza lika kwamitin ya ce za a yi amfani da wadannan bukukuwa a birnin na Nanjing, domin kara fahimtar da matasan duniya game da al'adun kasar Sin.

Bugu da kari za a gudanar da bikin nuna zane-zane na wasannin Olympics din tun daga ranar 18 zuwa 30 ga watan nan, inda za a gwada zane-zane fiye da 300, wadanda masu fasahar zane-zane daga kasashe da yankuna 78 na duniya suka yi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Tarihin wasannin Olympics 2013-08-01 20:18:10
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China