in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban kasar Sin ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Namibiya
2015-03-22 17:11:35 cri

Manzon musamman na shugaban kasar Sin kuma ministan kula da harkokin zirga-zirga na kasar Mr Yang Chuantang ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Namibiya tare kuma da bikin cika shekaru 25 da samun 'yancin kan kasar ta Namibiya da aka yi a birnin Windhoed babban birnin kasar, tare da ganawa da sabon shugaba Hage Geingob.

Yayin ganawar nasu, Mr Yang ya isar da kyakkyawan fatan shugaba Xi Jinping ga shugaba Geingob a ciki wannan rana ta musamman. Inda kuma ya ce, wannan shekara ta kuma cika shekaru 25 da kafa dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, Sin na fatan yin amfani da wannan zarafi mai kyau don kara hada kai da Namibiya, da zurfafa amincewa da juna a fannin siyasa da daga matsayin hadin gwiwa tsakaninsu, har ma da kara karfin samun daidaituwa kan harkokin kasa da kasa, da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar tsakaninsu ta yadda al'ummominsu gaba daya zasu amfana.

A nasa bangare, Mr Geingob ya darajanta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu sosai, tare da nuna godiya matuka ga tallafi da taimakon da Sin ke baiwa kasarsa cikin dogon lokaci, yana fatan kasashen biyu zasu cigaba da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a dukkanin fannoni.

An ba da labari cewa, manyan shugabanni da wakilai daga kasashe, yankuna ko kungiyoyi daban-daban kimani 50 suka halarci wannan kasaitaccen biki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China