Sabon shugaban kasar Namibiya Hage Geingob ya yi rantsuwar kama aikinsa a jiya Asabar 21 ga wata a birnin Windhoek hedkwatar kasar.
Yayin bikin rantsar da shi, Mr. Geingob ya gabatar da jawabinsa inda ya bayyana yaki da talauci da kawar da shi baki daya. Ya ce, a matsayinsa na shugaban kasar, zai tabbatar da wadata a kasa tare da yin kira ga jama'arsa da su hada kansu domin raya kasarsu tare.
Ranar 21 ga watan Maris, rana ce ta cika shekaru 25 da samun 'yancin kan kasar Namibiya. Hakan ya sa Geingob ya nuna godiya sosai ga taimakon da kasashen makwabtaka suka baiwa kasar wajen samun 'yancinta, a cewarsa kuma, Namibiya za ta dauki manufofin sada zumunci tare da sauran kasashe, kuma ba za ta nuna kiyayya ga sauran kasashe ba. (Amina)