Shugaban kasar Namibiya Hifikepunye Lucas Pohamba ya ce, ya kamata, jama'ar kasar su tuna da wasu kasashe kawayensu da suka goyi bayan gwagwarmayyar da kasar ta yi wajen neman samun 'yancinta.
Hifikepunye Pohamba wanda ya fadi hakan a cikin jawabin da ya karanta lokacin da ya halarci bikin ranar tunawa da jarumai ta kasar a ran 25 ga wata, ya bayyana cewa, kasashen Sin, Angola, Nijeriya, Zambiya, Libya, Masar, Aljeriya da dai sauran kasashe sun ba da gudunmawarsu ga gwagwarmayya da Namibiya ta yi, da ba don taimakon su, da kasar ba ta iya samun nasara cikin sauri ba, don haka ya kamata, a dinga tunawa da su a ko da yaushe.
Ita dai Namibiya ta samun 'yancin kanta ne a shekarar 1990 bayan ta fice daga Afrika ta kudu. Kuma an mai da ranar 28 ga watan Agusta ranar tunawa da jarumai da zummar tunawa da gwagwarmayya da suka yi daga arewacin kasar a ranar 26 ga watan Agusta na shekarar 1966. (Amina)