A yayin da yake tattaunawa da takwaransa na Namibia, Hifikepunye Pohamba, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, gwamnatin Nijeriya za ta dora muhimmanci kan batun yaki da ta'addanci, kuma ta riga ta yanke shawarar kara daukar matakai masu karfi, domin yaki da kungiyar Boko Haram dake arewa maso gabashin kasar Nijeriya. A don haka Shugaba Jonathan yayi fatan gwamnatin Namibia za ta ba da goyon baya da taimako a wannan fanni
Bayan haka, a yayin da wata ganawa da yayi da 'yan Nijeriya mazauna Namibia, shugaba Jonathan ya ce, ko da yake yanzu Nijeriya na fuskantar matsalar cin hanci da rashawa,duk da haka ana zuzuta wannan batu abin da ke yin babbar illa ga mutuncin jama'a da kasar Nijeriya.
.(Fatima)