Ta ce, tun da dadewa, jama'ar kasashen Sin da Namibia suna goyon bayan juna da fahimtar juna, sun kuma samu sakamako mai gamsarwa kan fannoni daban daban bisa hadin gwiwa da shawarwarin dake tsakaninsu. Gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali sosai kan bunkasuwar dangantakar kasashen biyu, wannan ya sa take son ci gaba da inganta dangantakar hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi, ta yadda zai tallafawa jama'ar kasashen biyu. (Maryam)