in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 5 ne suka mutu a sakamakon hadarin jirgin saman soja a Namibia
2014-04-13 16:40:36 cri
A Jiya Asabar 12 ga wata ne wani jirgin saman sojan kasar Namibiya ya yi hadari a birnin Grootfontein dake arewacin kasar, hadarin da ya haddasa rasuwar mutane 5, tare da jikkata ragowar biyar dake cikin sa.

Wata jaridar kasar ta labarta cewa, jirgin na hanyar sa ne ta zuwa birnin Windhoek, hedkwatar kasar. Ya kuma yi hadarin ne jim kadan da tashin sa.

Tuni dai ministan tsaron kasar ta Namibia Nahas Gideon Angula, ya mika sakon ta'aziya ga iyalai, da 'yan uwan wadanda hadarin ya ritsa da su. A hannu guda kuma an fara gudanar da bincike kan musabbabin aukuwar hadarin. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China