in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara babban zabe karo na biyar a Namibia
2014-11-28 14:38:16 cri
A ranar Jumma'a 28 ga watan nan ne, aka fara kada kuri'u a babban zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin Namibia karo na biyar, tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai.

Jam'iyyu 16 da 'yan takarar shugabancin kasar 9 ne dai suka shiga zaben na wannan karo, kuma wasu na ganin cewa babu shakka jam'iyya mai mulki ta SWAPO, da dan takarar ta Hage Geingob ne za su lashe zaben da gagarumin rinjaye. Idan dai har hakan ta tabbata, Hage Geingob zai kasance shugaban kasar na uku tun bayan samun 'yancin kan kasar a shekarar 1990.

A halin yanzu dai jam'yyar ta SWAPO na ci gaba da jaddada aniyarta ta yaki da talauci, da kyautata zamantakewar jama'ar kasa, da kuma samar da karin guraben ayyukan yi.

Har ila yau a wannan karo ana sa ran kasar ta Namibia, za ta kyautata fasahohinta da fannoni da dama, wannan ne kuma karo na farko da kasar za ta yi amfani da na'urorin zamani wajen gudanar da jefa kuri'a.

Masu jefa kuri'u a kasar dai su kusan miliyan 1.2, sun kunshi mazauna birane da karkara, ana kuma fatan za a kammala aikin zaben ta na'urorin kada kuri'u na lantarki a tashohin da aka kafa. A kuma halin yanzu, kwamitin kula da harkokin zaben kasar ya riga ya fara horas da jama'ar kasa, hanyar kada kuri'u ta na'urorin.

Haka kuma, shugaban sakatariyar kwamitin ya bayyana aniyar gudanar da harkokin zaben yadda ya kamata, ana kuma sa ran gabatar da sakamakon babban zaben a ranar 29 ga wata.

Rahotanni na cewa kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU, da gamayyar raya kudancin nahiyar Afirka ta SADC, da sauran kungiyoyin shiyya-shiyya za su aike da jami'an sa ido zuwa kasar ta Namibia domin lura da yanayin babban zaben kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China