Manufar kofin karramawar da ofishin jakadancin Sin da ke Namibia ya baiwa daliban da suka yi ficin, ita ce karawa daliban karfin gwiwar koyon harshen Sinaci da al'adun Sin.
A jawabinsa na bayar da lambar yabon,Farfesa Lazarus Hangula, mataimakin shugaban jami'ar Namibia ya ambaci wadannan dalibai a matsayin barade.
A halin yanzu akwai cibiyoyin koyar da harshen Sinanci na conficius guda 30 a Afirka da sama da 400 a sassa daban-daban na duniya.(Ibrahim)