Shugaban kasar Namibia Hifikepunye Pohamba ya bayyana a gun shawarwarin da ya yi tsakaninsa da Ban Ki-moon cewa, a matsayin membar MDD, kasar Namibia tana sa lura kan harkokin kasa da kasa da na yankuna, kana ta taka muhimmiyar rawa wajen hana yaduwar hamada, da batun tinkarar sauyin yanayi, da neman samar da daidaito a tsakanin jinsin maza da mata, da kiyaye zaman lafiya da bunkasuwa a kudancin Afirka da dai sauransu.
A nasa bangare, Ban Ki-moon ya yabi kasar Namibia game da nasarori da ta samu a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma bayan samun 'yancin kanta, kana ya yi godiya ga kasar bisa nuna goyon bayanta ga ayyukan MDD da sauki nauyin batutuwan dake shafarta. Ban Ki-moon ya kara da cewa, bayan da kasar Namibia ta samu 'yancin kai, ta gudanar da dukkan zabukan shugabanci ta cikin lumana, yana mai fatan za a ci gaba da kiyaye zaman lafiya a yayin zaben shugaban kasar dake tafe cikin watan Nuwanbar bana, kuma kasar za ta kara yin kokari wajen yaki da cutar kanjamau da kawar da talauci a nan gaba. (Zainab)