in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi babban zabe a Namibiya
2014-11-28 20:46:10 cri

A yau Jumma'a 28 ga wata, aka yi babban zabe karo na biyar a Namibiya tun bayan samun 'yancin kan kasar. A wannan rana, a rumfunan jefa kuri'a guda uku dake birnin Windhoek, hedkwatar kasar, wakilinmu ya yi hira da wassu manyan jami'ai uku na jam'iyyar SWAPO mai mulki yanzu,wato shugaba mai ci yanzu na kasar mista Hifikepunye Pohamba, da tsohon shugaban kasar na farko mista Sam Nujoma, da kuma dan takarar shugabancin kasar Hage Geingob, wadanda suka bayyana cewa, akwai dankon zumunci tsakanin Namibiya da Sin, a sabili da haka, za a ci gaba da zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Za a fitar da sabuwar majalisar wakilai da shugaban kasar a cikin wannan babban zabe, jam'iyyu 16 da 'yan takara 9 suke takara a wannan karon, inda masu jefa kuri'a sun yi amfani da na'urar kada kuri'a karo na farko. Kafofin yada labarai suna ganin cewa, jam'iyyar SWAPO dake rike da mulkin kasar da dan takara mista Geingob ne za su lashe zaben. Ana sanya ran cewa, za a gabatar da sakamakon babban zaben a gobe 29 ga wata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China