in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon firaministan kasar Lesotho ya yi rantsuwar kama aiki
2015-03-18 16:23:05 cri

Sabon firaministan kasar Lesotho Pakalitha Mosisili ya yi rantsuwar kama aiki a birnin Marcelo hedkwatar kasar. A cikin jawabinsa na kama aiki a lokacin bikin, Mosisili ya bayyana cewa, sabuwar gwamnatin za ta yi iyakacin kokarin tabbatar da hadin kan jama'a da zaman karko.

Mr Mosisili ya ce, muradin gwamnati a wannan zagaye shi ne tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar da kyautata zaman rayuwar jama'a. Ban da haka kuma, ya yi kira ga jama'ar kasa da su hada gwiwa da jam'iyyu daban-daban don cimma wadannan muradu.

Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma a matsayin wakilin kungiyar raya kudancin Afrika bai daya (SADC) ya halarci bikin.

A karkashin shiga tsakanin da SADC ta yi, Lesotho ta yi zaben majalisar dokoki shekaru biyu kafin wa'adinta ya cika, wato a ran 28 ga watan Fabrairu na wannan shekara da muke ciki da zummar kawo karshen rigingimu da aka tayi bisa dalilin bambancin ra'ayi tsakanin jam'iyyun daban-daban. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China