Rahotanni sun ce tuni Mr. Thabane ya tsallaka kasar Afirka ta Kudu, yayin da kuma a Lahadin nan rundunar sojin kasar da 'yan sanda suka yi musayar wuta ta tsahon sa'o'i uku, koda yake dai an ce ba a samu asarar rayuka ya yin musayar wutar ba.
Kaza lika rundunar sojin ta hana amfani da hanyoyin sadarwar gidajen radiyo, da na talebijin da dai sauransu.
Tuni dai firaministan kasar ta Lesotho ya tabbatarwa wani gidan talabijin dake kasar Afirka ta Kudu aukuwar juyin mulkin kasar ta sa. Ya kuma bayyana wa wani gida rediyon kasar Burtaniya cewa, zai tattauna da wasu shugabannin kasar Afirka ta Kudu, da ke wakiltar kungiyar bunkasa kudancin Afirka ta SADC kan yanayin da Lesothon ke ciki. Kana ya na fatan komawa gida da zarar an samu yanayi na tsaron lafiyar sa. (Maryam)