in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar 'yan adawa ta kasar Africa ta kudu ta bukaci gwamnatin kasar  data fayyace rawar da ta taka a rikicin Lesotho
2014-09-08 16:59:34 cri
Jam'iyyar hadakar Damokradiya 'yan adawa ta kasar Africa ta Kudu, ta bukaci gwamnatin Africa ta kudu da ta fito karara ta bayyana irin rawar da ta taka a rikicin kasar Lesotho.

Jam'iyyar 'yan adawar ta yi wannan kiran ne a daidai lokacin da ake samun rahotanni dake zargin cewar Africa ta kudu na da hannu a rikicin siyasar kasar Lesotho wanda ya barke a ranar 30 ga watan Agustan da ya gabata, a yayin da wani juyin mulki na sojojin Lesotho ya yi sanadiyyar sulalewar firaministan kasar Thomas Thabane zuwa Africa ta kudu.

To amma kuma firaminista na Lesotho, Thabane ya koma kasar tasa a ranar Litinin bayan da kungiyar raya kasashen kudancin Africa–SADC, suka shiga tsakani tare da jagorancin Africa ta kudu.

Rahotanni na zargin da cewar gwamnatin Africa ta kudu ta taka rawa kai tsaye ko kuma a asirce domin akwai yiwuwar ta tura rundunar tsaron kasar Africa ta kudu da kuma rundunar 'yan sanda ta kasar zuwa kasar ta Lesotho.

Ministan harkokin kasashen waje da gamayya Steven Mokgalapa ya ce jam'iyyar adawar na neman cikakken bayani daga gwamnatin ta Africa ta kudu. (suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China