in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SADC ta bukaci firaministan kasar Lesotho ya sake bude majalisar dokoki
2014-09-16 15:16:57 cri
Kungiyar raya kasashen kudancin Afirka ta SADC ta bukaci firaminstan kasar Lesotho Thomas Thabane ya sake bude majalisar dokokin kasarsa ba tare da wani bata lokaci ba.

Hukumar kula da harkokin siyasa da tsaro ta SADCn dai ta kara gudanar da wani taron gaggawa ne a daren ranar Litinin a birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu, inda aka tattauna kan halin da ake ciki a kasar ta Lesotho, da kuma kokarin da ake yi na daidaita rikicin siyasar kasar ta hanyar siyasa.

Wata sanarwar bayan taron da aka fitar a ranar Talatar nan ta nuna cewa, wajibi ne a sake bude majalisar dokokin kasar ba tare da wani bata lokaci ba, gabanin babban zaben kasar ta Lesotho, wanda kuma hakan zai taimakawa kokarin da ake yi na kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Kaza lika sanarwar ta yi kira ga hadaddiyar gwamnatin kasar Lesotho, da kungiyoyin siyasar kasar da su zage damtse wajen warware matsalolin dake addabar kasar bisa doka da oda, tare da cika alkawarin da suka dauka na maido da yanayin biyayya ga doka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China