in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Lethoto yana bukatar zaman lafiya kafin sake bude majalisar dokokin kasar
2014-09-15 20:31:39 cri
Firaministan kasar Lethoto Thomas Thabane ya ce, sai an mai do da zaman lafiya a kasar kafin ya sake bude majalisar dokokin kasar.

Mr. Thabane ya bayyana haka ne ta kafar talabijin na eNCA a Lethoto gabanin taron kolin kungiyar SADC da aka shirya gudanar wa yau Litinin a Pretoria na kasar Afirka ta kudu da nufin cimma yarjejeniya tsakanin sassan kasar ta Lethonto da ke rikici da juna.

A baya dai an shirya bude majalisar dokokin kasar ce a ranar 12 ga watan Satumba,amma firaministan ya gaza cimma wannan yarjejeniya saboda abin da ya kira rashin kwanciyar hankali a kasar.

Wannan lamari shi ne ya tilasta wa shugaba Jacob Zuma na Afirka ta kudu kana shugaban kula da harkokin siyasa da tsaro na kungiyar ta SADC kiran taron gaggauwa na shugabannin shiyyar kan yadda za a warware wannan matsala.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China