in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu wani zaman taron majalisar dokoki sai idan an dawo da zaman lafiya, in ji faraministan Lesotho
2014-09-21 16:50:43 cri
Faraministan kasar Lesotho, Thomas Thabane ya bayyana a ranar Asabar cewa majalisar dokokin kasar ba za ta sake yin wani zaman taro ba idan har zaman lafiya da kwanciyar hankali ba su dawo ba cikin kasar.

"Ina bisa kariyar rundunar sojojin kasar Afrika ta Kudu, kuma wannan yana nufin cewa kowa ba ya cikin zaman lafiya a cikin kasar," in ji mista Thabane a yayin zaman jana'izar wani ofisan 'yan sanda.

Mokheseng Ramahloko, mai shekaru 52 da haifuwa, ya mutu bayan sojojin kasar sun harbe shi da bindiga a ranar 30 ga watan Agustan da ya gabata a Maseru, hedkwatar kasar a lokacin da suka kai samame a hedkwatocin 'yan sandar kasar.

Lesotho, kasa ce da kasar Afrika ta Kudu ta kewaye ta fuskanci wani yunkurin juyin mulki a ranar 30 ga watan Agusta dalilin sabanin dake tsakanin 'yan sanda da rundunar sojojin kasar.

Ta wani bangare, shugabannin gamayyar ci gaban kasashen kudancin Afrika da na hadakar Lesotho sun bayyana cewa gaggauta yin zabubuka zai iya taimakawa wajen maido da tsarin demukaradiya da zaman lafiya a cikin wannan kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China