Yayin taron gaggawa da kungiyar SADC ta gudanar a birnin Pretoria dake kasar Afirka ta Kudu a wannan rana, Thabane ya bayyana cewa, yanzu ana fuskantar zaman dar-dar a kasar ta Lesotho, don haka kamata ya yi kungiyar SADC ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar don kwantar da hankali a kasar. (Zainab)