in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori daban daban na kasar Lesotho sun kara yin alkawarin warware rikicin kasar cikin lumana
2014-09-10 15:32:22 cri
A ranar 9 ga wata, bangarori daban daban na hadaddiyar gwamnatin kasar Lesotho sun ci gaba da sulhuntawa a karkashin shiga-tsakanin shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma. A lokacin tattaunawar sun yi alkawarin warware rikicin siyasa na kasar cikin lumana, da maido da odar kasar.

Bayan tattaunawar mai tsawon awoyi uku, firaministan kasar Lesotho Thomas Thabane, da mataimakin firaministan kasar Mothetjoa Metsing, sun amince da ci gaba da gudanar da shawarwari kan yadda za a warware rikicin kasar, kuma za su tabbatar da lokacin sake bude majalisar dokokin kasar kafin ranar 12 ga wata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China