in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin firaministan kasar Lesotho ya fara mulkin rikon kwarya
2014-08-31 20:31:26 cri
Mataimakin firaministan kasar Lesotho Mothetjoa Metsing ya fara jagorantar gwamnatin rikon kwarya, bayan da firaminista Tom Thabane ya tsere zuwa Afirka ta Kudu, sakamakon jiyun mulkin da sojoji suka aiwatar a kasar.

Ministan sadarwa, kimiyya da fasaha na kasar Selibe Mochoboroane, ya bayyana wa manema labaru cewa, fara jagorantar kasar da mataimakin firaministan ya yi ya dace da tsarin mulkin kasar.

Da safiyar jiya Asabar ne bisa agogon kasar ta Lethoso, sojoji suka kai farmaki gidan firaminista Tom Thabane, tare da kwace hedkwatar jami'an tsaron kasar, da wani ofishin 'yan sanda dake Maseru, fadar mulkin kasar.

Matakin da ya tilastawa mista Thabane tsallakewa zuwa Afirka ta Kudu, bisa taimakon wasu dakarun musamman na kasar, kamar dai yadda jaridar Sunday Times ta Afirka ta Kudu ta rawaito.

Sai dai a daya hannun sojojin kasar ta Lesotho sun musunta zargin da aka yi musu na gudanar da juyin mulki. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China