in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Lesotho ya tsaida kudurin dage sake bude majalisar dokokin kasar
2014-09-09 15:32:08 cri
Firaministan kasar Lesotho Thomas Thabane, ya sanar da dage sake bude majalisar dokokin kasar sakamakon tsanantar yanayin da ake ciki a kasar sa.

Kaza lika a ranar Litinin wani kakakin Mr. Thabane ya bayyana cewa, dalilin jinkirta bude majalissar na da alaka da burin da ake da shi, na gudanar da bincike kan wanda ke da iko da sojojin kasar.

Yarjejeniyar sulhu kan rikicin kasar Lesothon da aka cimma a ranar 1 ga watan nan, ta kunshi alkawarin da Mr. Thabane ya yi na sake bude majalisar dokokin kasar a ranar 19 ga wata, wadda aka rufe tsawon watanni 3.

A daya hannun kuma gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta sanar da cewa shugaban kasar Jacob Zuma zai ziyarci Lesotho a Talatar nan, domin shiga-tsakani game da rashin jituwa dake akwai tsakanin bangarorin kasar.

A ranar 30 ga watan Agusta da ya shude ne dai sojojin kasar Lethoso suka mamaye babban ofishin 'yan sanda dake birnin Maseru, da kuma fadar shugaban kasar, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan sanda, kafin daga bisani firaminista Thabane ya arce zuwa kasar Afirka ta Kudu.

Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta ce shugaban kasar Zuma, zai ziyarci kasar Lesotho a Litinin din nan da nufin shiga-tsakani, tare da burin jan hankulan bangarori daban daban da rikicin ya shafa, da su aiwatar da yarjejeniyar sulhu da aka cimma a ranar 1 ga watan nan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China