A hirar da yayi da manema labarai a wannan rana Mr Phooko yace ya zama mukaddashin Firaminista kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Wannan sanarwa dai yazo ne bayan da Firaministan kasar Thomas Thabane ya tsera zuwa kasar Afrika ta kudu a safiyar asabar sakamakon wani yunkurin juyin mulki da sojoji suka so aiwatarwa.
Mataimakin Firaministan, Mothejoa Metsing shima ya isa kasar ta Afrika ta kudu a safiyar lahadi domin halartar taron kungiyar kasashen gabashin Afrika a bangaren siyasa,ayyukan Soji da kuma tsaro domin samar da mafita game da rikicin da ake fuskanta a kasar shi.(Fatimah Jibril)