Rundunar sojojin kasar sun killace hedkwatar 'yan sanda, in ji Thesele Maseribane, ministan wasannin motsa jiki kana shugaban jam'iyyar Basotho National Party a wata hirarsa da 'yan jarida.
Kamfanin dillancin labarai na South African Broadcasting Corporation (SABC) ya ambato wani ofisa a cikin hedkwatar 'yan sanda na cewa an killace su.
Mista Maseribane ya ambato wani yunkurin juyin mulki a cikin wannan karamar masarauta da kasar Afrika ta kudu ta kewaye. Haka kuma sojojin sun dakile hanyoyin sadarwa na rediyo. Amma duk da haka, ministan ya jaddada cewa gwamnatin kasar tana bisa ikonta.
Faraministan kasar Thomas Thabane da ni kaina muna cikin gwamnatin hadaka. Faraminsta yana kan ikonsa kuma yana cikin koshin lafiya, in ji mista Maseribane.
Kaftan Ntlele Ntoi, kakakin rundanar sojojin Lesotho ya bayyana cewa sojojin sun dauki wannan matakin bayan sun samu bayanan dake nuna cewa wasu ofisoshin 'yan sanda suna shirin mikawa wani gungun 'yan siyasa na kusa da faraminista makamai da harsasai. (Maman Ada)