in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu ci gaba sosai a hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika ta fuskar ciniki da tattalin arziki
2015-03-18 10:59:31 cri
Kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Shen Danyang ya bayyana cewa kasar Sin da Afrika sun samun ci gaba sosai wajen hadin gwiwa a fannin ciniki da tattalin arziki tsakanin su a cikin shekarun baya-baya.

Yayin da yake amsa tambaya game da cinikayyar da ke tsakanin Sin da Afrika, a wata ganawa da manema labaru a nan birnin Beijing Mr Shen ya yi bayanin cewa, a shekarun baya, Sin da Afrika sun samun ci gaba mai armashi a wannan fanni. Yawan kudin cinikin dake cikin sassan biyu ya karu da kamanin kashi 30 bisa 100, hakan ya sa Sin ta zama abokiyar ciniki ta farko ga Afirka a wannan fanni cikin shekaru shida a jere. Kayayyakin yau da kullum da kasar Sin ta kera na samu karbuwa sosai a kasuwannin Afrika, kuma kayayyakin kasashen Afrika na kara shiga cikin kasuwannin kasar Sin. Ban da haka kuma, yawan kudin da Sin ke zubawa Afrika na karuwa matuka. Haka zalika, Mr Shen ya ce, wannan shekara ta cika shekaru 15 da kafa dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika, kuma za a kira taron ministoci karo na shida na dandalin a kasar Afrika ta kudu a karshen wannan shekara.

Yace Sin kuma za ta ci gaba da rike ka'idojin hadin gwiwa da kasashen Afrika, musamman ma ta fannonin ayyukan gina manyan ababen more rayuwa ciki hadda dogon layoyin jiragen kasa da na motoci masu saurin tafiya, da bangaren zirga-zirga ta jiragen sama, a sa'i daya kuma za ta kara hadin gwiwa da kasashen Afrika wajen tsai da sabbin manufofi a fannonin hada-hadar kudi, kawar da talauci, kiyaye muhalli, yin mu'ammala a fannin al'adu da sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China