Kasar Sin na sa ran za a cimma nasarar gudanar da bikin tunawa da cika shekaru 60 da taron Bandung, kuma tana fatan za'a ci gaba da bin manufar Bandung a halin yanzu da sa kaimi ga samun bunkasuwar nahiyar Asiya da Afrika gaba daya.
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana hakan a yau Alhamis 12 ga wata yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, game da yadda wani jami'in diplomasiyya na kasar Indonesiya ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu shugabannin kasashe 17 suka tabbatar da halartar bikin da za a yi a karshen watan Afrilu mai zuwa a kasar.
Mr Hong ya ce, an kira taron Bandung a shekarar 1955 a kasar Indonesiya wanda ya kasance karo na farko da kasashen dake Asiya da Afrika suka gudanar da wani taron kasa da kasa cikin hadin gwiwarsu, abin da ya zama wani babban mataki a tarihin dangantakar kasa da kasa. A cewarsa, Sin na ci gaba da goyon bayan hadin gwiwa a tsakanin kasashen Asiya da Afrika, tare da kiyaye zaman lafiya da karko da samun bunkasuwa gaba daya a nahiyoyin biyu. (Amina)