Merkel ta bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Jumma'a 20 ga watan nan, yayin taron koli na kungiyar EU da aka yi a birnin Brussels. Da take tsokaci kan rahoton neman taimakon da shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya gabatar wa EU kuwa, Merkel ta nuna cewa, kasarta ba za ta samar da kudi ba, har sai lokacin da EU ta halarci matakan sojin da kasar Faransan ke dauka a nahiyar ta Afirka. Merkel ta kara da cewa, ba abu ne mai yiwuwa ta bada kudade, ba tare tabbatar da halarcin harkokin sojin da Faransa ke gudanarwa ba. A hannu guda ta nuna amincewarta da matakan sojan da Faransan ke dauka a wasu kasashen dake nahiyar ta Afirka.
Bugu da kari, babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Anders Rasmussen, da kuma shugaban majalisar dokokin kungiyar EU Martin Schulz, dukkansu sun amince da ra'ayin madam Merkel. (Maryam)