in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afirka da su yi amfani da kimiya don farfado da ayyukan noma
2015-02-24 16:49:26 cri
Kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta yi kira ga gwamnatocin kasashen nahiyar da su yi amfani da hanyoyin kimiya domin farfado da bangarensu na aikin gona.

Kwamishinar kungiyar mai kula da tattalin arzikin yankunan karkara da aikin gona Rhoda Peace Tumusiime wadda ta bayyana hakan yayin taron dandalin aikin gona da ya gudana a birnin Nairbobi na kasar Kenya ta ce, duk wani ci gaba da aka samu a duniya, an same shi ta hanyar kimiya da fasahar kere-kere

Don haka ta ce, kamata ya yi nahiyar Afirka ta ba da muhimmanci ga irin rawar da harkar kimiyya ke takawa muddin tana son inganta harkar aikin gona

Ta ce, amfani da kayayyakin noma na zamani zai taimaka wa kananan manoma, musamman mata da matasa wajen ganin su ma ba a bar su a baya ba a kokarin da ake na samar da abinci a nahiyar.

Tumusiime ta ce, musayar bayanai ta hanyar amfani da wayoyin salula na baya-bayan nan kan yadda za a inganta aikin noma wani mataki ne da ya zo a kan gaba. Kana ta bayyana muhimamncin yin hadin gwiwa da sassa masu zaman kansu a wannan banngare.

Kungiyar ta AU ta ayyana shekarar 2014 a matsayin shekarar aikin noma, da samar da abinci mai gina jiki, sannan ta himmatu wajen ganin an kawar da yunwa a nahiyar ya zuwa shekarar 2025.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China