in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka na amfana daga jarin da Sin ke zuba wa kan ababan more rayuwa
2015-02-24 16:50:35 cri
Masana tattalin arziki daga nahiyar Afirka sun bayyana cewa,nahiyar tana amfana matuka daga irin jarin da kasar Sin ke zuba wa a bangaren samar da muhimman kayayyakin more rayuwa kamar hanyoyin mota,jiragen kasa da kuma wutar lantarki.

Wannan bayani na kunshe ne cikin wata hira da Elly Twineyo, wani masanin tattalin arziki kana mawallafin littafin nan mai suna "dalilan da suka durkusar da Afirka" ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua. Yana mai cewa, galibin tallafin da kasashen yammacin duniya suka baiwa nahiyar, tallafi ne da suka shafi tsara manufofi,tafiyar da gwamnati ko horas da ma'aikata, sabanin irin tallafin da Sin ke baiwa bangaren raya muhimman kayayyakin more rayuwa, wadanda jari ne na dogon lokaci da zai yi tasiri mai muhimmanci.

Don haka ya bukaci kasashen na Afirka da su mayar da hankali kan tallafin raya kasa yayin da za su sabunta hadin gwiwar tattalin arziki da kasar ta Sin.

Ya ce, wasu sassan da ke ciwa nahiyar tuwo a kwarya su ne, sufuri da makamashi, kuma rashin su sun takawa nahiyar birki a kokarin da ta ke na janyo masu sha'awar zuba jari kai tsaye daga ketare.

Bayanai na nuna cewa, yanzu haka kamfanonin kasar Sin na aikin gina hanyoyi da samar da makamashi a sassa daban-daban na nahiyar. Misali a gabashin Afirka, Sin na daukar nauyin gina hanyar jirgin kasa daga garin Monbasa mai tashar jiragen ruwa zuwa Nairobi, babban birnin kasar Kenya,ana kuma saran hade kasashe dake makwabtaka da ita kamar Uganda,Rwanda da Sudan ta kudu.

Bugu da kari Sin tana gina tashar samar da wutar lantarki kasashen Uganda,Habasha da wasu sassan nahiyar a kokarin da ta ke na magance matsalar makamashin da ke shafar ci gaban masana'antun nahiyar ta Afirka.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China