Ban da haka, za su samar da gatanci ga masu yawon shakatawa na kasashen ketare ta hanyar samar da sabuwar takardar izni ta bai daya. An ce, wannan takardar izni za ta kara hadin gwiwa tsakanin kasashen uku.
Ministan kula da kananan hukumomi na kasar Ruwanda Mussoni ya nuna maraba ga sauran kasashe biyu daga cikin EAC wato Tanzaniya da Burundi da su shiga wannan shiri.
Masu yawon shakatawa na kasashen ketare suna iya shiga da kuma ratsa wadannan kasashen uku sau da dama cikin watanni 3 bisa wannan sabuwar takardar izni wadda ta bukaci a biya kudi dala dari daya.
Shugaban hukumar yawon shakatawa da tsaron kasar ta kwamitin raya kasar Ruwanda ya nuna cewa, yana fatan kamfanoni masu zaman kansu da za su yi amfani da wannan zarafi mai kyau domin zuba jari kan sha'anin yawon shakatawa. (Amina)