Mista Wang ya kara da cewa, yayin ziyararsa a wannan karo a kasar Sudan, an mai da martani kan kiran da Sin ta yi na gudanar da taron goyon bayan shawarwarin da kungiyar IGAD ta yi don shimfida zaman lafiya a Sudan ta kudu, a ganinsa, kasashen Afrika na amincewa da kasar Sin a siyasance, ba ma kawai suna fatan kara hadin gwiwa da kasar Sin a fannin tattalin arziki ba, kuma suna fatan kasar Sin zata kara ba da gudunmawarta wajen warware batutuwan Afrika dake jawo hankalin kasa da kasa, da tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro a Afrika.
Ban da haka kuma, Mista Wang ya ba da amsa kan tambayar cewa, ko akwai wani canji da aka samu kan matakin da Sin ke dauka kan aikin diplomasiyya, ya ce, Sin ta kan tsayawa tsayin daka kan kiyaye kwanciyar hankali da tsaro. Tun shekaru 50 na karni 20, Sin ta shiga tsakanin batun yankin Cine na kasar Indiya da Faransa ta mamaye, ban da haka kuma, Sin ta shiga tsakanin rikicin Combodia a shekaru 80, har ma ta shiga shawarwari tsakanin bangarorin shida kan batun nukiliyar Korea ta Arewa a shekaru 90. A matsayin wata kasa mai girma, ya kamata Sin ta dauki nauyin dake wuyanta don kiyaye zaman lafiya, a sa'i daya kuma, kamata ya yi Sin ta yi kokarin neman wata hanya mai halin musamman dake dacewa da halin da Sin ke fuskanta da kuma warware wasu batutuwa dake jawo hankalin kasa da kasa. (Amina)