Rundunar Sojin kasar Afrika ta kudu, ta musanta wani rahoto dake cewa ta turawa kasar Najeriya sojoji domin tallafawa yakin da ake yi da 'yan Boko Haram.
Kakakin sojin Afrika ta kudun Siphiwe Dlamini, ya ce kasar sa ba ta taba tura sojojin ta Najeriya ba. Kaza lika Dlamini ya ce duk wani dan Afrika ta kudu da ya shiga aikin dakile mayakan Boko Haram a Najeriya, za a dauke shi a matsayin sojan-haya, matakin da zai sanya shi gurfana gaban koliya sakamakon saba wa dokar kasar sa.
Wasu kafafen watsa labaru dai sun fidda wasu rahotanni dake cewa Najeriyar ta yi hayar daruruwan sojoji daga Afirka ta Kudu, domin yaki da 'yan Boko Haram. An ce an gano wasu sojojin Afirka ta kudun na sintiri a titunan birnin Maiduguri hedkwatar jihar Borno dake Arewa Maso gabashin Najeriyar. (Amina)