Tun daga ofishin jakadanci har zuwa dandalin kasa, dake tsakiyar birnin N'Djamena hedkwatar kasar Chadi, daruruwan 'yan kasar Kamaru, a karkashin jagorancin jakadan kasar Kamaru da ke kasar Chadi, mista Ba Oumarou Sanda, suka fito domin nuna yabo ga hadin gwiwar Chadi da Kamaru kan yaki da kungiyar Boko Haram da kuma kara baiwa rundunonin sojojin kasashen biyu kwarin gwiwa domin kawar da wannan kungiyar ta'addanci daga kasashen Chadi da Kamaru. Haka kuma masu jerin gwanon sun bayar da taimakon abinci ga wadannan sojojin dake yakin kare 'yanci.
Wannan wani mataki ne na nuna hadin kai da goyon baya, da kuma nuna kauna tsakanin kasashen biyu, in ji janar Ndoubayo Marc, mashawarcin musamman na hedkwatar rundunar sojojin kasar Chadi.
Hukumomin kasar Chadi sun amince, a cikin watan Janairun shekarar 2015, wajen tura sojoji zuwa kasashen Kamaru da Najeriya dake makwataka da kasar domin taimaka masu yaki da kungiyar Boko Haram.
Boko Haram dai ta fara kai hare harenta a cikin jahohin Najeriya, kafin kuma ta fadadasu zuwa makwabtan Nijeriya, lamarin da ya kasance babbar barazana ta fuskar tsaro ga kasashen Kamaru, Nijar da Chadi. (Maman Ada)