in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Nigeriya an fara shari'ar manyan jami'an soji akan kin yarda su yaki boko haram
2015-03-10 21:07:54 cri
A wannan makon aka fara zaman shari'a na wassu janar din soji biyu da wassu jami'an sojin guda 20 akan zargin da aka masu kwanan nan cewa sun ki amincewa da umurnin yaki da kungiyar boko haram, kungiyar 'yan ta'adda da suka zama ma kasar karfen kafa.

Kamar yadda wata sanarwa daga hukumar tsaron sojin kasar ta fitar a Talatan nan, an ce wadanda ake zargin an tuhume su ne da laifin cin amanar kasar ko kuma yi ma rundunar tsaron kasar zagon kasa wadanda da farko an yi shari'a ma wadansu rukunonin sojojin har biyu da aka zarge su da irin wannan laifin.

Sojojin dai da suke sauraron laifinsu, sun bayyana cewa sun bukaci a basu taimako ne na kayan aiki ba wai sun ce ba za su yaki kungiyar ba. Rukunonin biyu da aka yi shari'ar su a baya an yanke masu hukuncin kisa ta hanyar harbe su a karshen shekarar bara a wata shari'ar sojin da aka yi a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China