Makasudin wannan taro, shi ne bullo da dabarun sadarwa na hadin gwiwa a wannan lokacin da ake yaki da kungiyar Boko Haram, da kasashen biyu ke yaka ba kakkautawa tun yau da kwanaki da dama yanzu.
A cikin jawabinsa, ministan sadarwar Nijar, Yahouza Sadissou ya bayyana cewa wannan zaman taro ya zo kwanaki kadan bayan ziyarar aiki da abokantaka da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya kai a birnin N'Djamena, inda kuma ya samu tattaunawa tare da takwaransa na Chadi, Idriss Deby Itno kan batutuwan karfafa huldar dangantaka tsakanin kasashen biyu, shiyyarsu da ma Afrika baki daya. Haka kuma ya kara da cewa wannan taro na gudana a cikin wani yanayin tsaro da ke halaka da yaki da mayakan kungiyar Boko Haram da ke janyo tashe tashen hankali a wasu yankunan dake kewayen tafkin Chadi.
Minista Yahouza Sadissou, ya bayyana cewa a karkashin jagorancin Issoufou Mahamadou da Idriss Deby Itno, sojojin Nijar da Chadi sun sami nasarori sosai kuma suna kan hanyar murkushe mayakan kungiyar Boko Haram.
A nasa bangare, ministan sadarawan Chadi kuma kakakin gwamnatin Chadi Hassan Bakari Silla, ya bayyana cewa zuwansu Nijar nada nasaba da halin da ake ciki da ya shafi tun yau da 'yan kwanaki game da matsalar yaki da Boko Haram a yankin tafkin Chadi. A ganinsa matsalar 'yan ta'adda da ke zubar da jinin al'ummomi, ta shafi kasashen da ke kewayen tafkin Chadi sosai. Gaban wannan hadari dake kasancewa babbar barazana ga kasashen, sun dauki matakan gaggawa kuma da karfi na tura jami'an tsaro cikin hadin gwiwa tsakanin kasashen Chadi, Kamaru, Nijar da Najeriya domin yaki da kungiyar Boko Haram in ji mista Bakari Silla. (Maman Ada)