Kwamitin tsaro na MDD ya yi kira da a cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Mali
Kwamitin tsaro na MDD ya yi kira a ranar Jumma'a ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da rikicin kasar Mali ya shafa da su nuna imaninsu da tunani mai zurfi domin taimakawa ga kai ga cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya a kusantowar sake komawa teburin shawarwarin shimfida zaman lafiya tsakanin gwamnatin kasar Mali da 'yan tawaye a kasar Aljeriya.
Za'a sake fara shawarwarin shimfida zaman lafiyar a ranar Lahadi a birnin Alger domin kai ga cimma wata yarjejeniya daga dukkan fannoni da kuma za ta yi la'akari da bukatun kowane bangare domin cimma wata mafita ga rikicin kasar Mali, in ji kwamitin tsaro na MDD da ke kunshe da mambobi goma sha biyar a cikin wata sanarwar da mika wa 'yan jarida a ranar Jumma'a da yamma. (Maman Ada)