Muna cikin wani shirin da babu ja da baya. Shiri ne na zaman lafiya da dukkan bangarorin da abin ya shafa suka amince da shi, mista Ould Sidi Mohamed tare da jaddadawa kan girmama yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma dakatar da ayyukan takalo fitina domin ida aiwatar da wannan shiri da ya kusa kawo karshensa.
A yau, dukkan 'yan kasar Mali sun maida hankalinsu kan wannan shirin kuma nuna fatan cimma mafita daga wannan rikici in ji ministan tare da yin kira ga kungiyoyi masu dauke da makamai dasu kaucewa shiga tashe tashen hankali jawo fitina, har da dukkan bangarorin dake fagen daga domin girmama yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Muna cikin wani shirin cimma wata yarjejeniya, magana ce ta nan da 'yan makwanni, ina son tuni mu tattara burin neman sulhu, wannan wani shiri ne na sake maido da yarda da juna. Domin wannan batu ba za'a iyar warware shi ba illa kawai ta hanyar yin shawarwari in ji Ould Sidi Mohamed. (Maman Ada)