in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta amince da binciken da aka yi ga na'urorin sojin kasar Sin masu kiyaye zaman lafiya a kasar Mali
2014-11-25 11:09:14 cri
A ranar 24 ga watan nan ne jami'an MDD suka gudanar da bincike kan na'urorin soji rukuni na biyu, na sojojin Sin masu aikin kiyaye zaman lafiya dake kasar Mali.

Wannan ne dai karo na farko da tawagar musamman ta MDD dake kasar Mali ta yi bincike kan karfin rukunin na biyu na sojojin Sin dake kasar Mali a dukkan fannoni.

Bayan kammala binciken na su a birnin Gao, jami'an MDDr su 4 sun bayyana cewa, dukkan kayayyaki, da na'urori da karfin gudanar da ayyuka na rukunin sojojin Sin masu kiyaye zaman lafiya dake kasar Mali, sun dace da bukatun MDD, kuma MDDr ta amince da sakamakon binciken da aka yiwa rukunin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China