in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Shaolin na kasar Sin sun baiwa shugaban kasar Mali kyaututtuka
2014-11-09 16:48:38 cri
'Yan buddah na Shaolin na kasar Sin da ke ziyara a kasar Mali sun baiwa shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita kyaututtuka a yayin da yake halartar wani bikin nuna wasan Shaolin na kasar Sin a ranar Asabar a birnin Bamako . 'Yan buddah na dakin ibadar Shaolin suna a kasar Mali tun daga ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata a cikin tsarin bunkasa zaman lafiya. Kyaututtukan da 'yan buddah suka baiwa shugaban Mali, wadanda suka sosa masa rai sun hada da wani littafin dake kunshe da arzikinsu da kuma wani zanen hoto dake martaba bunkasa zaman lafiya da kawar da nuna karfin tuwo.

Wannan zanen hoto wani irin kwatancinsa na wani dandamalin dake cikin dakin ibada a kasar Sin da kuma ke bayyana hadin kai da hakuri da juna tsakanin yankuna da jituwa a cikin al'umma, a wani bayanin da ya fito daga bikin nuna wasan. Bayan wadannan 'yan buddha, matasan kasar Mali su ma sun nuna fasahohinsu da suka faranta ran shugaban kasar Mali dake bayyana wata makoma ga 'yan kasar Mali na fatan ganin an kafa wata makarantar Shaolin a kasar Mali. Hakan na cikin tsarin yadda kome ke gudana, kuma bisa tsarin abokantaka mai zurfi dake tsakanin al'ummomin kasar Sin da Mali in ji shugaban kasar Mali. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China