in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan shugabannin kasar Sin sun halarci tarukan wakilan jama'ar kasa na NPC
2015-03-06 11:12:04 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran zaunannun mambobin ofishin siyasa, na kwamitin tsakiyar JKS sun halarci zaman tattaunawa kan rahoton aiki na gwamnatin kasar da firaminista Li Keqiang ya bayar jiya Alhamis 5 ga wata, tare da wakilan jama'ar kasar da ke halartar taron shekara-shekara na NPC.

Yayin da shugaba Xi ya halarci zaman tattaunawa na wakilan birnin Shanghai, ya jaddada cewa, sa kaimi ga aikin kafa yankin ciniki cikin 'yanci, daya ne daga muhimman matakai cikin sabon tsarin bude kofa ga kasashen waje. Ya ce ya kamata a kara wayar da kan mutane, da mai da aikin yin kwaskwarima kan tsare-tsare, a matsayin babban matakin inganta kwazo da sa kaimi ga samun bunkasuwa.

Ban da haka, Mr. Xi ya kara da cewa, kamata ya yi a kara kyautata tsare-tsare, da gano sabbin dabaru a fannin hada-hadar kudi, a kokarin kara karfin ba da hidima ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, tare da rarraba jari a duniya.

Mamban dindindin na ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Mr. Wang Qishan shi ma ya halarci zaman tattaunawa na wakilan birnin Beijing, inda ya yi nuni da cewa, daukar tsauraran matakai kan ayyukan jam'iyya, mataki ne babba na kafa harshashin gudanar ayyukanta yadda ya kamata.

Ya kara da cewa kamata ya yi a maida hankali kwarai ga aiwatar da ka'idojin jam'iyya, da kayyade ikon shugabanni. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China