Yayin taron, wakilai kimanin 3000 sun sauke nauyin dake kan su bisa tsarin mulkin kasa da doka, kuma sun zartas da wasu rahotanni ciki hadda rahoton aikin gwamnati, inda suka takaita ci gaba, da darussa da aka samu a cikin shekarar da ta gabata a dukkan fannoni, tare kuma da gabatar da sababbin ayyuka da za a yi a wannan shekara da muke ciki. (Amina)