in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a zurfafa yin kwaskwarima a dukkanin fannoni tare da dora muhimmanci kan wasu fannoni, in ji firaministan Sin
2014-03-13 13:14:50 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, kamata ya yi kasar Sin ta zurfafa yin kwaskwarima a dukkanin fannoni, tare da dora muhimmanci kan wasu fannoni kebantattu, a kokarin da ake yi na samun bunkasuwar wasu muhimman fannoni.

Mr. Li ya bayyana hakan ne ga mamema labaru na gida da na waje yau Alhamis a nan birnin Beijing, bayan rufe taro karo na 2 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12.

Firiaminstan na kasar Sin wanda kuma ya amsa tambayoyin manema labarun, ya kuma yi karin haske kan matakan da za a dauka, dangane da yadda za a samu ci gaba a yayin da ake aiwatar da kwaskwarima.

Li ya ce, an zurfafa yin kwaskwarima ne a dukkanin fannoni, yayin cikakken zaman taro karo na uku na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na 18, wato yin kwaskwarima a fannoni daban daban na bunkasa tattalin arziki, zamantakewar al'umma da dai sauransu.

Ban da haka, Li ya kara da cewa, bana za a ci gaba da dora muhimmanci kan amfani da kasuwanci, da yin kwaskwarima ga sashen haraji da hada hadar kudi, da kyautata tsari ta hanyar yin kwaskwarima ga manufofi, domin zurfafa yin gyare-gyare ga kamfanoni mallakar kasa, a kokarin kara karfin kasuwanni, na yin takara a fannonin kiwon lafiya, da hada-hadar kudi da dai sauransu.(fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China