in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana da kwarewa da ikon tafiyar da harkokin tattalin arziki yadda ya kamata, in ji firaminista Li Keqiang
2014-03-13 13:11:24 cri

Firaministan kasar Sin Mista Li Keqiang, ya ce Sin, ta samu fasahohin tinkarar raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki da aka yi fama da shi bara, haka kuma tattalin arzikinta na da makomar bunkasuwa nan gaba.

Mr. Li wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarun da aka shirya a yau, bayan rufewar taron shekara-shekara karo na biyu, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12, ya kuma ce kasar ta Sin, tana da kwarewa, da kuma ikon tafiyar da habakar tattalin arzikin ta yadda ya kamata a shekarar nan da muke ciki.

An shirya wannan taron ne dai bayan rufewar zaman shekara-shekara karo na biyu, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12 a wannan rana. A yayin da yake ba da amsa kan tambayar da aka yi masa game da babban kalubale da ya fi tsanani wajen tinkara a shekara daya, da ya yi a matsayin firaministan kasar Sin, Mista Li ya ce, babban kalubale da ya fuskanta mafi tsanani shi ne, na raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki, inda wasu ra'ayoyin bainal jama'a na kasashen duniya suka rika hasashen cewa, watakila saurin karuwar tattalin arzikin Sin zai ragu cikin sauri, wata kila ma yawan karuwarsa ya yi kasa zuwa kashi 3 ko 4 bisa dari kacal.

Game da haka, Li ya ce, mun samu nasara wajen tinkarar wannan matsala, har ma mun cimma babban burin ci gaban bunkasuwar tattalin arzikinmu, da ingantar zaman takewar al'umma da muka sanya gaba.
Li ya kara da cewa, a bana, ana ci gaba da fuskantar babban kalubale, wanda mai yiyuwa ne zai fi yawan sauyawa bisa na bara. Amma idan an iya tinkarar matsalolin da ake fuskanta yadda ya kamata, za a iya samun nasara wajen bunkasa tattalin arziki a shekarar ta 2014.(Danladi)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China