Mpana ya kara da cewa.. "Tafiya ce mai nisa amma ta kayatar da mu. Game da yadda wannan ziyara ta gudana, da gudummawar 'yan jarida dake tare damu. A gaskiya abinda muka gani ya burge mu matuka. Lallai kasar Sin ta himmatu wajen neman karbar bakuncin wannan gasa. Kuma duk da cewa bamu san kuri'un da ragowar kasashe zasu jefa ba, a matsayin mu na jakadu, muna yiwa kasar Sin fatan alheri bisa wannan bukata."
Tun dai ranar 3 ga watan Nuwambar shekarar 2013 ne kwamitin neman wannan gasa na kasar Sin ya mikawa kwamitin IOC takardun sa, kaza lika cikin watan Yulin bara IOC ya zabi birnin Beijing a matsayin daya daga biranen da suka cancanci shiga takara, kana birnin na Beijing ya mika nasa takardun shiri ga IOC a watan Janairun da ya gabata.