in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guangzhou Evergrande ya sabunta kwangilar da ya kulla tare da dan wasan Brazil Elkeson
2015-03-04 09:48:20 cri
Dan wasan kasar Brazil Elkeson Cardoso ya kulla wata sabuwar kwangila ta tsawon shekaru 4 tare da shahararren kulob din wasan kwallon kafa na kasar Sin Guangzhou Evergrande, kamar yadda kulob din ya sanar a ranar Lahadin da ta gabata. A cewarsa, wa'adin sabuwar kwangilar zai kai ranar 28 ga watan Fabrairu.

Elkeson mai shekaru 25 a duniya, ya fara buga wasan a kulob din na Evergrande ne a shekarar 2012, inda ya ciwa kulaf din kwallaye 24, matakin da ya sanya shi zama dan wasa mafi ciwa kulaf din kwallaye, a gasar matakin kwararrun 'yan wasa ta kasar Sin CSL a shekarar 2013.

A kakar wasa ta 2014 kuwa, Elkeson ya sake cin kwallaye 28 a wasannin da ya buga, matsayin da ya sanya shi zama dan wasan mafi samar da gudunmowa wato MVP a tsarin gasar CSL din.

Bayan da ya samu sabunta kwangilarsa, Elkeson ya bayyana farin cikinsa a shafin yanar gizo na kulob din Evergrande, inda ya ce birnin Guangzhou da kulob din yake, ya riga ya zama tamkar gida a gare shi, kuma yana da fatan kara samun lambobin yabo a shekaru 4 masu zuwa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China