in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ivory Coast ta shiga zagayen karshe na gasar AFCON
2015-02-05 16:50:30 cri

A shirin yau za mu ci gaba da mai da hankali kan gasar cin kofin kwallon kafan nahiyar Afirka wato AFCON, gasar da a yanzu ke mataki na karshe, wato wasannin kusa da na karshe.

Da farko bari mu duba sakamakon wasan da ya gudana jiya Laraba tsakanin DR Congo da Ivory Coast. Sakamakon dai ya nuna yadda Ivory Coast ta doke janhuriyar dimokaradiyyar Congo da ci 3 da 1. Yanzu haka dai ta tabbata Ivory Coast ce za ta buga wasan karshe da ko dai Ghana ko kuma Equatorial Guinea, a ranar 8 ga watan nan na Fabarairu. Bayan Ghana da E/Guinea sun buga wasan su na semi-finals a ranar Alhamis din nan.

Idan mun waiwayi tarihin wannan gasa, za mu ga cewa da fari kasar Morocco ce ya kamata ta karbi bakuncinta, kafin daga bisani ta kauracewa hakan dalilin tsoron bazuwar cutar Ebola a kasar, matakin da ya sanya Equatorial Guinea ta zamo mai masaukin gasar, wanda hakan kuma ya bata damar samun tikitin buga gasar, ta kuma shirya cikin watanni 2 kacal kafin fara buga gasar ta Afcon.

Wani abun lura ma shi ne duk da cewa kasar Equatorial Guinea ba wata babbar kasa ba ce, idan mun duba yawan al'ummarta ma basu wuce dubu 680 ba, kuma ba wata kasa ce mai karfin tattalin arziki ba. Amma a hakikanin gaskiya ta taka rawar gani wajen cimma nasarar wasannin dake wakana. Sanin kowa ne dai wasannin da ake bugawa na tafiya yadda ya kamata ba tare da gamuwa da wata matsala ba. Kuma kamar yadda hukumar AFCON da kungiyar AU da sauran hukumomin yankunan Afirka suka yi hasashe tun da fari, babu wanda ya kamu da cutar Ebola sakamakon halartar gasar dake daf da kammala. Kana ba a samu wani tashin hankali ba.

Yanzu haka ana jinjinawa Equatorial Guinea kwarai, bisa yadda ta fito, ta dauki nauyin gudanar da wannan gasa, haka kuma ganin yadda kungiyar kasar ta nuna karfin ta gasar, har ma ta kai wasan kusa da na karshe a karon farko. A nan ina ga ya dace mu kalli wasan ranar Asabar, wanda ya ba Equatorial Guinea damar kaiwa wasan daf da na karshe, inda ta doke kasar Tunusia da ci 2 da 1.

Nasarar da Equatorial Guinea ta samu a wannan karo dai ita ce irin ta ta farko, tun bayan da shekarar 2012, ta samu kaiwa ga wasan kusa da na kusan karshe.

Ya yin wasan da ya gudana a ranar Asabar da ta wuce, dan wasan Equatorial Guinea Javier Angel Balboa ne ya ciwa kasar ta sa kwallaye biyu, ta farko a minti na 90, ta bugun daga kai sai mai tsaron gida, sai dai da yake kafin hakan Tunusia ta riga ta samu nasarar jefa kwallo guda ta hannun dan wasan ta Akaichi cikin minti na 71, an tashi wasan kunnen doki 1 da 1.

Kuma a cikin karin lokacin da aka yi ne Angel Balboa na Equatorial Guinea, ya jefa kwallo ta biyu a zaren Tunusia. Haka kuma aka tashi wasan na birnin Bata 2 da 1.

Tunisia wadda ta nuna matukar kwarewa, ta taka leda yadda ya kamata, kuma da dama daga masu nazarin game da yadda wasan zai kasance na da tunanin ita ce za ta samu nasarar lashe wasan, kafin sakamakon karshe ya nuna akasin hakan.

Sai dai fa wannan wasa ya bar baya da kura, domin kuwa tuni hukumar dake shirya gasar wato CAF ta dakatar da alkalin wasan Rajindraparsad Seechurn har tsahon watannin 6, tare da cin sa tarar dala 50,000, bisa laifin busa fenaretin da ya baiwa Equatorial Guinea nasarar lashe wasan ba bisa ka'ida ba.

Irin yanayin alkalancin da ya yi ya harzuka 'yan kallon kasar Tunusia, wadanda suka auka cikin filin wasan bayan an hura tashi.matakin da ya sanya cin tarar kasar Tunisia dala 50,000, za kuma ta biya kudin kayan da magoya bayan ta suka barnata a filin wasan na Bata. Ta kuma gabatar da takardar ba da hakuri ga hukumar.

Ita ma Equatorial Guinea an ci ta tarar dala 5,000.

Tuni kuma CAF din ta bayyana rashin jin dadin ta game da yadda alkalin wasan ya busa wancan wasa.

A daya wasan kuma kasar Ghana, wadda ita ma kungiya ce mai karfin gaske a fannin taka leda, ita ma kuma ana mata zaton lashe wannan gasa da ake bugawa. Wani abun lura ma shi ne yadda tauraron dan wasan ta Kwesi Appiah ke hasakawa sosai a bana. Appiah dai na buga kwallo ne a rukuni na biyu na ajin kwararru a kasar Birtaniya, kuma a farkon watan da ya gabata aka sanya shi cikin kungiyar kasar Ghana, a matsayin daya daga 'yan wasan kasar ajin farko, ya yin wasan Ghana da kasar Guinea.

Ya yin wannan wasa Kwesi Appiah ya nuna matukar kwarewarsa, ya taimaka wajen kai hare-hare ga kasar Guinea, tare da taimakawa abokan wasan sa jefa kwallo ta farko a ragar Guinea mintuna 4 da take wasan. Har wa yau Appiah ya jefa kwallon ta farko a ragar Guinea, bayan da dan wasan kasar ya yi kuskuren sakin kwallon dake kafarsa. Kafin dai a tashi wasan Ghana ta jefa kwallon ta ta 3 a ragar Guinea, aka kuma tashi Ghanan na da kwallo 3 Guinea na nema.

Bisa rawar da ya taka wajen baiwa Ghana gudummawa ya yin wannan wasa Appiah ya samu yabo, inda aka zabe shi matsayin zakaran wasan na ranar Asabar.

Kwesi ya sanya wasu hotuna kan shafin sa na twitter, wadanda suka nuna yadda yake kallon wasan da kasar sa ta buga shekaru 4 da suka wuce, da yadda ya sanya rigar kungiyar Ghana a wannan karo a matsayin daya daga 'yan wasan kasar ta sa, ya kuma rubuta cewa 'Duk wanda ke neman cimma buri, sai ya cika alkawarin da ya dauka, kafin cikar burinsa"

An haifi Appian ne a Thamesmead dake birnin London, ya kuma kammala wata kwalejin kwallon kafa dake birnin a shekarar 2008.

Appiah ya bugawa kananan kulaflika da dama kwallo, kamar su Peterborough, da Weymouth, da King's Lynn da kulaf din birnin Kettering.

Sauran sun hada da kungiyar kwallon kafar birnin Brackley da Margate. Sai kuma Crystal Palace a shekarar 2012, da kulaf din birnin Yeovil da Cambridge United.

Ya kuma koma Notts a ranar watan Janairun bara, a watan Maris kuma ya koma AFC Wimbledon, inda ya buga kakar wasa ta 2013 zuwa 14.

Appiah ya samu cikakkiyar damar bugawa kasashen Ghana da Ingila wasa. A kuma ranar 24 ga watan Disambar bara aka kiya shi domin shiga jerin 'yan wasa 31 da zasu wakilci kasar Ghana a gasar cin kofin Afirka dake daf da kammala yanzu haka.

Wannan dan wasa kamar yadda muka bayyana ya taka rawar gani ya yin wasannin da Ghana ta buga, da farko a wasan kasar da Afirka ta Kudu, wasan da Ghanan ta lashe da ci 2 da 1. Sai kuma kwallon da ya ciwa Ghanan a wasan su da Guinea.

Ban da wannan kuma kasar Sin ita ma ta ba da taimako ga aikin watsa bidiyon wasannin a telabijin. Da ma, babban ginin cibiyar gidan telabijin ta kasar Equatorial Guinea TVGE, kasar Sin ce ta gina shi kyauta a shekarar 2006, kuma cibiyar ce cibiyar yada shirye shiryen telabijin mafi girma a kasar, inda ake amfani da na'urorin zamani wajen aiki.

Haka kuma akwai wata tawagar kwararru Sinawa masu fasahar daukar bidiyon telabijin, wadda take aiki a cibiyar telabijin din domin ba da taimako a fannin fasaha. A wannan karo, yayin da gidan telabijin din na kasar Equatorial Guinea TVGE ke kokarin watsa bidiyon gasar cin kofin Afirka kai tsaye, kwararrun ma'aikata Sinawa dake wurin sun ba da taimako sosai, ta hanyar lura da na'urori, da tabbatar da gudanar yada shirye-shirye yadda ya kamata.

Mu koma ga tarihin wannan gasa, gasar an fara gudanar da gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka ne a shekarar 1957, kuma kasar Masar ce la lashe kofin na wannan shekara, bisa kididdiga gasar dake gudana a bana itace ta 30.

Kuma kasashen da suka fi daukar kofin gasar sun hada da kasar Masar wadda ta dauka sau 7, sai Ghana da Kamaru wadanda suka dauka sau 4, Najeriya ta dauka sau 3, ya yin da janhuriyar dimokaradiyyar Congo ta dauka sai 2.

Sauran kasashen da suka taba daukar wannan kofi sau dai-dai sun hada da Cote d'Ivoire, da Aljeriya, da Zambia, da Morocco da Tunusia da Habasha da Sudan da Congo da kuma Afirka ta Kudu.

Idan mun kalli wannan sakamakon muka kuma alakanta shi da kasashen da suka rage a gasar ta bana, ma iya cewa Equatorial Guinea ce kawai bata taba daukar wannan kofi ba. Ya yin da masu fashin baki da dama suke zatawa Ghana ko Cote d'Ivoire daukar kofin na bana.(Saminu Alhassan/Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China