in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi jana'izar babban jami'in wasanni na kasar Sin mista He Zhenliang
2015-01-15 14:46:42 cri
A ranar Asabar din da ta gabata ne wasu gungun 'yan wasa, da jami'an hukumar wasannin kasar Sin, gami da wasu jama'a Sinawa suka halarci bikin jana'izar He Zhenliang, tsohon mambar a kwamitin Olympics na kasa da kasa IOC, kuma mataimakin shugaban kwamitin, wanda ya taimakawa kasar Sin wajen samun damar karbar bakuncin wasannin Olympics na shekarar 2008. Marigayi He Zhenliang ya rasu ne a ranar 4 ga watan nan a birnin Beijing, bayan ya sha fama da rashin lafiya yana da shekaru 85 a duniya.

An gudanar da bikin jana'izar sa ne a wani wuri dake kusa da kaburburan Babaoshan dake yammacin Beijing, bikin da aka fara tun daga karfe 10 na safe, aka kuma kwashe awa 1 ana gudanar da shi. Mutanen da suka halarci bikin sun hada da uwargidan Thomas Bach, shugaban kwamitin Olympics na kasa da kasa, da mambar kwamitin zartaswa na IOC Wu Ching-kuo, gami da wasu manyan jami'an kwamitin IOC.

A madadin shugaban IOC Bach, Timothy Tsun Ting Fok, wanda shi ma ya kasance wani mamba a hukumar IOC, ya jajantawa iyalan marigayi He Zhenliang kafin fara bikin jana'izar.

A nashi bangaren, Bach na hukumar IOC ya bukaci a sassauto da tutar IOC zuwa rabin sandarta tsawon kwanaki 3 masu zuwa, don nuna girmamawa ga marigayi He. A cewar Bach, He ya kasance mutum da ya san darajar al'adu, wanda ya taimakawa yaduwar ra'ayin da ya shafi wasanni, gami da kokarin sanya kwamitin IOC fahimtar kasarsa ta Sin, da jama'ar ta, gami da al'adunta masu muhimmanci. Yau kwamitin Olympics ya rasa daya daga cikin jakadunsa mafi kuzari da zafin nama, in ji mista Bach.

A nan kasar Sin, an fi sanin mista He Zhenliang da lakabin ' Mista Olympics', bisa la'akari da yadda aka zabe shi don shiga cikin kwamitin Olympics na kasa da kasa a shekarar 1981, sa'an nan ya zama mataimakin shugaban kwamitin a shekarar 1989, inda ya yi shekaru 4 yana aiki a wannan matsayi.

Wani abu ma da ba za a manta ba shi ne, yadda marigayin ya taka muhimmiyar rawa a kokarin sanya birnin Beijing zama birnin da ya karbi bakuncin wasannin Olympics a shekarar 2008, bayan da birnin ya nemi samun wannan dama amma ba tare da samun nasara ba shekaru 8 da suka wuce.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China