Rahotanni sun nuna cewa bisa shirin, za a fara sayar da tikitin da yawansu ya kai miliyan 7 da dubu 500 tun daga watan Maris mai zuwa.
Bisa kuma burin baiwa jama'a damar kallo wasannin na Olympics, farashin tikiti miliyan 3 da dubu 800, daga jimillar tikitin da za a sayar a wannan karo, ba za su kai kudin Brazil Real 70 ba. Kaza lika tsofaffi, ko nakasassu, da kuma dalibai na da damar sayen tikitin da rabin farashin sa.
Za dai a gudanar da wasannin Olympics na shekarar 2016 a birnin Rio de Janeiro ne, tun daga ranar 5 zuwa 21 ga watan Agustar shekarar ta 2016, kuma wannan ne karon farko da za a gudanar da wasannin na Olympics a nahiyar kudancin Amurka. (Zainab)