"Akwai dalilai da yawa da suka sanya kasar Sin maida hankali game da wannan batu, na farko akwai bukatar da al'ummar mu ke da ita. Musamman Sinawa na kara nuna sha'awar su ga harkokin wasanni, kuma masu shiga manyan gasannin motsa jika suma suna karuwa, a gabar da hankula ke komawa ga yadda za a kara kiyaye lafiyar jiki ta hanyar wasanni da motsa jiki. Sai dai duk da haka wasannin lokacin sanyi basu shahara sosai a wasu yankunan Sin ba, tun shekarar 2006 da Sinawa suka kalli wasannin lokacin sanyi, suke kara nuna sha'awar su ga wannan harka. A nan Beijing kadai akwai kulaflikan wasan kwallon gora ta kankara na 'yan firamare har 2000, suna kuma gudanar da wasanni tsakanin su. Ya yin da Sinawa da dama ke zuwa zhangjiakou domin shiga irin wadannan wasanni na kankara. Don haka burin al'ummar mu ne muhimmin dalili da ya sanya mu maida hankali kan harkar neman karbar bakuncin wannan gasa ta shekarar 2022".